Sabon kawancen 'yan adawa na yamutsa hazo a Benin
November 13, 2024Wannan ba shi ne karon farko da aka fara aiwatar da irin wannan yunkuri na neman kare dimukaradiyya a kasar Benin ba, a daidai lokacin da ake tunkarar zaben shugaban kasar da zai gudanar a 2026. Ko da shekarar 2021, jam'iyyun adawa sun hada gwiwa wajen kafa wata hadaka mai suna Les Democrates don sa ido kan yanayin shirya zabe da gudanar da shi. Sai dai, matsaloli irin daban-daban sun kunno kai musamman ma hamayya a tsakanin shugabanni, lamarin da ya raunana tafiyar ta hanyar dare hadakar gida biyu ko ma fiye da haka.
Joel Atayi Guèdègbé, da ke sharhi kan harkokin siyasar Jamhuriyar Benin, ya ce barakar da ta faru a baya za ta iya sake kunno kai a wannan karon inda ya ce "Akwai rigingimu na jagoranci, wanda ya kamata a yi tunani a kai. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin adawa da mulkin Shugaba Talon ne kawai jam'iyyun siyasar suka sa a gaba, ko kuma bayan haka, wadannan kungiyoyi da ke shelanta kan su a matsayin 'yan adawa za su iya rikidewa zuwa wata madogara da za ta iya kwace mulki a hannun gwamnatin da take cewa ta gaza?Zabuka na gaba ne kawai za su yi bambance dan duma da kabewa."
Karin Bayani : Benin: Kokarin sasanta rikici da Nijar
Sabanin gamayyar jam'iyyun adawa na baya, wannan tsarin tuntuba da ake wa lakabi da "Cadre de concertation" na zuwa ne kasa da shekaru biyu kafin zaben shugaban kasar Benin. Amma Gilles Goyi, memba a majalisar koli ta jam'iyyar UPR, wacce ke cikin kawance da ke mara wa shugaban kasa baya, ya ce bai ga wata manufar kirki da ke cikin wannan hadaka ta adawa ba.
"A kan wadanne batutuwa ne ake son tuntubar juna, idan aka duba abin da suka kira manyan ayyuka, da ke zama ginshikin damuwarsu? Wannan ba daidai ba ne, saboda duk batutuwan da aka yi tsokaci a kansu sun zama maimai kawai, saboda duk matsaloli ne da aka riga aka magance su. Misali, sake kwaskare ka'idojin zabe, batu ne da aka magance tun da dadewa."
'Yan adawan Jamhuriyar Benin da dama na daure a gidan yari, lamarin da ke kawu nakasu wajen aiwatar da yunkurin hada karfi da karfe da nufin inganta yanayin shugabanci a nan gaba. Sai dai Joel Atayi Guèdègbé da ke sharhi kan lamarun siyasa, ya yi imanin cewa shirin tuntubar juna zai iya kawo fata a fannin dimukaradiyya saboda zai iya zama silar lashe zabubbuka masu zuwa. Amma ya ce sai a mutunta sharadin hadin kai ne tukuna kwalliyar wannan gamayyar za ta biya kudin sabulu.
Karin Bayani :Rikici ya ki cinyewa tsakanin Talon da Janar Tiani
"Ana iya samun hadin kai, ko hobbasa don shafe duk abin da ba shi da kyau ko da ke hana ruwa gudu, tare da ba wa kai damar samun nasara. Amma kuma a daya bangare, akwai yiwuwar samun rarabuwar kawuna da zai iya dare hadakar gida barkatai. Kuma kowa ya kwana da sanin cewar, idan babu hadin kai, akwai kasadar iya shan kaye, ma'ana a kasa yin tasairi a rumfunan zabe. Don haka kalubale ne babba ta wannan mahanga. Kalubale ne na hadin kai."
'Yan adawa na kasar Benin na sane da wannan kalubale na rashin zama tsintsiya madaurinki daya, bisa la'akari da manufofin da suka a gaba na tuntubar juna don cimma muradin samun sauyin shugabanci a lokacin babban zaben 2026.