1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawar da ta'adanci a kasashen kewayen tafkin Chadi

Ubale MusaOctober 7, 2014

A cigaba da kokarinsu na neman dakile tada kayar baya ta masu kaifin kishin addini, shugabannin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi na wani taro a Nijar don samawa kansu mafita.

Verteidigungsminister der Mitgliedsstaaten von CBLT
Hoto: DW/M. Kanta

A baya dai shugabannin wadannan kasashe sun gudanar da taruka makamantan wannan a birnin Paris na Faransa da Ndjamena a Chadi duka dai da nufin ganin an lalubo hanyoyin da za bi wajen ganin an girka zaman lafiya a kasashen da ke gefen tafkin Chadi wadanda wannan matsala ta shafa, musamman ma rikicin Boko Haram da a 'yan shekarun nan ya addabi tarayyar Najeriya da wasu sassa na Jamhuriyar Kamaru da ke makotaka da Najeriyar.

Rikicin Boko Haram ya addabi Najeriya da makotanta.Hoto: AP

Babban burin shugabannin da ke gudanar da wannan taro dai shi ne samar da runduna ta hadin gwiwa mai karfi da za ta kai ga farautar 'yan kungiyar Boko Haram da ke watse a cikin kasashen. Ana dai bukatar daruruwan miliyoyi daloli don kaiwa ga cimma burinsu na samar da wannan runduna to sai dai wani abu da ke zaman kalubale garesu shi ne karanci kudi da wasunsu ke fama da shi.

Wata matsala kuma da suke fuskanta da ka iya gurgunta wannan yunkuri nasu shi ne irin rauni na shugabanci da ake samu a kasashen Afirka kamar dai yadda Dr. Kole Shettima na cibiyar Mc Arthur Foundation ya shaida. Wannan magana da Dr. Shettima ya yi ne ma ya sanya da dama ke ganin sai an hada karfi da karfe wajen tunkarar matsalar muddin ana son ganin bayanta.

Dr. Jibrin Ibrahim na cibiyar Raya Demokaradiya da Mulki na Gari na daga cikin masu tunanin sai a tashi tsaye ba babba ba yaro wajen fuskantar wannan tada kayar bayan masu kaifin kishin addini duba da yadda rikicin ya tashi daga kisa da sace talakawa zuwa sace manyan mutane da ma neman hallakasu kamar yadda aka gani lokacin da 'yan Boko Haram suka sace matar mataimakin firaministan Jamhuriyar Kamaru a kwanakin baya.

Tada kayar bayan 'yan ta'adda ta haifar da samun 'yan gudun hijira da yawa.Hoto: picture alliance/AP Photo

Yanzu haka dai masu fashin baki kan sha'anin tsaro da kuma wadanda ke sanya idanu kan harkokin yau da kullum a wadannan kasashe na zuba idanu don ganin yadda wannan taro da ke wakana a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar zai yi tasiri wajen cimma burukan shugabannin kasashen da ke hallartasa da ma talakawan kasashen da suke mulka wanda ke ciki fargaba ba dare ba rana saboda gudun abinda ka je ya komo.