1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mulki har abada a Chadi?

Mouhamadou Awal Balarabe SB
September 17, 2025

Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da kudirin doka da ke wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima , da ke tsawaita wa'adin mulkin shugabanci kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai.

Shugaba Mahamat Idriss Deby na Chadi
Shugaba Mahamat Idriss Deby na ChadiHoto: Mouta/AP/picture alliance

A kasar Chadi, majalisar dokoki ta amince da kudirin doka da ke wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima, da ke tsawaita wa'adin mulkin shugabanci kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai. Sannan ya tanadi tsawaita wa'adin 'yan majalisa na kasa. Sai dai 'yan adawa da dama sun kaurace wa zaman kada kuri'a saboda suna adawa da wannan mataki.

Mafari

Da farko dai daftarin kwakware kundin tsarin mulkin kasar Chadi da aka gabatar ya shafi babi na 77 ne kawai, wanda ke haramta wa shugaban kasa jan ragamar jam'iyyar siyasa, kafin daga bisani a fadada shi zuwa wasu batutuwa da dama. Hasali ma dai, daftarin da majalisa ta amince da shi ya tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasa daga shekaru biyar zuwa bakwai, wanda sau daya ne kawai za a iya sabunta shi.

Shugaba Mahamat Idriss Deby na ChadiHoto: Israel Matene/REUTERS

Sannan ya fadada wa'adin 'yan majalisar daga shekaru biyar zuwa shida, tare da ba da damar samar da mukami na mataimakin firaminista.

François Djekombé, shugaban jam'iyyar USPR da ke kawance da gwamnatin Chadi, ya bayyana wannan gyara ga kundin tsarin mulki a matsayin ci-gaba mai ma'ana.

Masu adawa majalisar dokokin

Majalisar dokokin ChadiHoto: Isouf Sanogo/AFP

Sai dai 'yan majalisar wakilai da aka zaba karkashin jam'iyyar RNDT-Le Réveil da madugun 'yan adawa Albert Pahimi Padacké ke jagoranta sun fice daga zauren majalisar domin nuna rashin gamsuwa da shirin kwaskware kundin tsarin mulki. Dalili, kuwa shi ne, ba a jima da amincewa da kundin tsarin mulkin kasar Chadi ba a lokacin da shugaban da ke ci a yanzu yake shugabancin gwamnatin mulkin soja. 

Bayani game da zaben Chadi

01:46

This browser does not support the video element.

Ga masanin kimiyyar siyasa Evariste Ngarlem Toldé, wannan yanayin siyasa da ake ciki yana share fagen yin wa jaririyar dimukuradiyyar Chadi rauni.

Duk da suka da wannan kudirin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki ya sha, amma majalisar dokokin Chadi ta amince da shi a karatu na biyu ba tare da wahala, saboda jam'iyyar da ke mulki da kawayenta na da rinjaye a majalisar.