1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Ukraine: Jirgin yakin F-16 daga kawaye

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 20, 2023

Kasashen Holand da Denmark sun sanar da aniyarsu ta bai wa Ukraine jiragen yaki kirar F-16, abin da shugaban Ukraine din ya ayyana da matakn bai wa sojojinsa kwarin gwiwa a yakin da take da makwabciyar kasa Rasha.

Ukraine |  Volodymyr Zelenskyy | Yaki | Rasha
Shugaban Ukraine Volodymyr ZelenskyyHoto: ROB ENGELAAR/AFP

Da ama dai Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya jima yana godon samun wadannan jiragen yaki kirar F-16 din daga kawayensa na Turai, domin kara karfin sojojin kasarsa. Ba da jimawa ba ne dai, Amurka ta bai wa Holland da Denmark din damar bai wa Ukraine jiragen yakin kirar kasarta. Kasashen biyu sun bayyana aniyar bayar da jiragen yakin ne, yayin ziyarar da Zelenskyy ya kai musu kana kwana guda bayan wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai a wani gidan kallo ya halaka mutane bakwai tare da raunata kimanin 150 ciki har da kananan yara.