WHO: Babu cutar polio a Afirka
August 27, 2020Talla
An dai jima ana fatan ganin an kawo karashen cutar polio lko kuma shan inna a fadin duniya. Yayin da tuni aka yi bankwana da kwayar cutar a wasu kasashe, a wasu kasashen kuwa da ke nahiyar Afirka da kuma yankin Asiya, an ci gaba da fama da wannan cuta.
Sai dai nahiyar Afirka ta samu nasarar shiga cikin nahiyoyin da suka yi bankwana da cutar ta polio, bayan da a wannan makon Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ayyana kawo karshen wannan cuta a nahiyar baki daya.
Najeriya na daga cikin kasashen da suka kasance kurar baya, wajen kawo karshen wannan cuta da ke yin illa ga yara kanana, musamman ma 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa.