1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kazakhstan za ta tura danyen mai Jamus

Binta Aliyu Zurmi
February 22, 2023

A gaba a yau ake sa ran kason farko na danyen mai daga kasar Kazakhstan zai isa kasar Jamus ta bututun karkashin kasa na Rasha a cewar kafar yada labaran Rasha ta RIA.

Ungarn Szazhalombatta | Druschba-Pipeline
Hoto: Attila Kiskbenedek/AFP/Getty Imgaes

Ministan makamashi na Kazakhstan Bolat Akchaulakov ya ce yana fatan komai ya tafi daidai a yau.

Makamashin na kasar Kazakhstan zai maye gurbin wanda Jamus ke saye daga Rasha ne tun bayan takunkumai da kasashen yamma suka kakaba wa Rasha bayan mamayar Ukraine da ya dakatar da shigar da man kasar zuwa kasashen yamma.

Danyen man da zai bi ta bututun nan na Druzhba wanda ya fi kowane girma a duniya wanda kuma baya cikin takunkuman da ke kan kayayakin kasar Rasha.

Wannan dai shi ne karon farko da manyan tashoshin tace danyan mai da ke Jamuus za su karbi danyen mai ta wannan bututun.