1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciNajeriya

Mece ce makomar ilimin yaran da aka sako a Kebbi?

November 26, 2025

A cikin wani dan kwarya-kwaryan biki, gwamnatin jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya ta mika wa iyayen daliban makarantar sakandiren kwana ta garin Maga yaransu 24 da 'yan ta'adda suka saki bayan kwashe su a makarantarsu.

Najeriya | Tsaro | 'Yan Bindiga | Makaranta | Dalibai | Yara
Yadda jami'an tsaro ke gadin wasu makarantu a Najeriya saboda rashin tsaroHoto: Sunday Alamba/AP Photo/dpa/picture alliance

'Yan makarantar sakandiren ta Maga sun gabatar da kansu yayin da ake mika su ga iyayensu, a cikin wani yanayi na ban tausayi kan taskun da yaran mata masu kananan shekaru suka shiga. Lamarin satar 'yan makarantar bai tsaya a kan yaran ba kawai, hatta da iyayensu mata ma ba su sami sukuni ba.

Iyaye da sauran al'umma sun yi farin ciki

Sai dai labarin sako yaran nasu ya saka su cikin murna, inji Malam Iliyasu Maga da aka dauke masa yara hudu ringis. Mai martaba sarkin Zuru yankin masarautar da abin ya faru, Alhaji Muhammad Sanusi Mika'il ya ce a matsayinsu na iyayen kowa, ba za su bar al'amarin ya dakushe karsashin yaran na ci gaba da karatu ba.

Katsina: Shin rufe makarantu ne mafita?

02:57

This browser does not support the video element.

Abu na gaba dai a halin yanzu shi ne makomar karatun yaran, wanda Farfesa Halima Bande da ke zama kwamishiniyar ilimi ta jihar ta ce akwai tanadi: "Wannan abu bai sa mun sare mun yi tanadi na musamman. Maganar tsaro wajen sauya wa yaran wurin zama domin kara ingata tsaro ga dalibai, don haka ilimi za a ci gaba da bayar da shi kuma dalibai za su samu ilimi."        

Raba yara da fargaba da firgici

Sai dai kwamishiniyar ilimin ta jihar Kebbi ta ce, kafin mayar da yaran makaranta cikin takwarorinsu sauran dalibai, sai an yi kokarin raba su da firgicin da ke tattare da su sakamakon kwanakin da suka dauka a hannun 'yan binidigar bayan sun sace su.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani