1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Keir Starmer na Labour zai zama sabon firaministan Burtaniya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 5, 2024

Firaminista mai barin gado Rishi Sunak ya amince da shan kayi har ma ya dauki alhakin zama silar faduwar jam'iyyarsa

Hoto: Suzanne Plunkett/REUTERS

Jagoran jam'iyyar Labour a Burtaniya Keir Starmer na shirin zama sabon firaminista,bayan da jam'iyyarsa ta lashe zaben da aka gudanar ranar Alhamis da gagarumin rinjaye, wanda ya kawo karshen shekaru 14 na mulkin jam'iyya mai ra'ayin rikau ta Conservative.

Karin bayani:Al'ummar Burtaniya na zaben 'yan majalisun dokoki

Firaminista mai barin gado Rishi Sunak ya amince da shan kayi, har ma ya dauki alhakin zama silar faduwar da jam'iyyarsa ta yi a zaben, yana mai cewar zai mika mulki lami lafiya, kuma yana yi wa sabbin shugabannin da aka zaba fatan alheri.

Karin bayani:Sadiq Khan ya sake lashe zaben magajin birnin London

Sabon firaministan mai jiran gado ya sha alwashin samar da sauyin ciyar da Burtaniya gaba, amma ya yi togaciyar cewa kada a yi zaton fara ganin sauye-sauyen nan take, domin abu ne da ke bukatar lokaci.

Gabanin kammala fitowar dukkan samakon zaben, yanzu haka dai Labour tana da kujeru 410 na 'yan majalisu, yayin da Consevatives ke da 117.

Tuni kungiyar tarayyar Turai EU ta taya Mr Starmer murnar lashe zabe, tare da fatan yin aiki tare da gwamnatinsa da zai kafa, kamar yadda shugaban majalisar EU din Charles Michel ya wallafa a shafinsa na X.