Kenya da Najeriya za su kawar da ta'addanci
January 27, 2016Shugabannin sun bayyana haka ne a lokacin fara ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ke yi a kasar ta Kenya wacce ta rasa rayukan jami'anta da dama a yayin da su ke aiyukan wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya. Wasu rahotanni dai a kasar ta Kenya na cewa a ranar Laraban nan ma an samu bayanai da ke nuna cewa wasu 'yan sanda sama da biyar sun rasa rayukansu bayan motar su ta taka nakiyar da ake zaton 'yan ta'adda ne suka dasa.
Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya ce 'yan ta'adda a kasar ba za su samu kwanciyar hankali ba don kuwa hukumomi sun tashi haikan wajen kawarsu kuma za us cigaba da ganin sojinsu sun samu goyon bayan da suke bukata Shi ma dai shugaba Muhammu Buhari da ke nasa tsokacin kan yaki da 'yan ta'adda wadanda ko a ranar Laraban nan 'yan Boko Haram sun kai farmaki da halaka mutane da dama a garin Chibok ya ce batun sararawa a yaki da ta'addanci a duniya bai ma tasoba.
A share guda shugaban Kenya ya ce akwai bukatar da ke akwai wajen hadin kai da mahukuntan Somaliya da sauran kasashe don yaki da 'yan ta'adda ciki kuwa har da na Al-Shabaab wanda Kenya din ke kan gaba wajen yaka. Wannan ne ma ya sanya Shugaba Kenyatta din ya ce ''ayyukan ta'addanci ba su da shamaki da abota ko kabila ko addini kwata-kwata''.