Kenya: Kotu ta yanke wa mutane uku hukuncin kisa
July 19, 2017Talla
A tun shekara ta 2014 ne dai wadanda aka yanke wa hukuncin ke zaman wakafi na jiran sakamakon shari'a, wannan hukuncin dai shi ne irin sa na farko cikin shekaru 30 a Kasar kenya, inda kasar tav gaza cimma zartar da hukuncin kisa kai tsaye a tun shekara ta 1987 sai dai hukuncin daurin talala a gidan yari.
Mai gabatar da karar ta shedawa kotu cewa mutanen uku na cikin mutane bakwai da suka farma ta a cikin motar kasuwa da nufin yi mata fyade, amma ta kubuta ne bayan da ta ce musu tana dauke da cutar Aids. Sai dai mutanen uku da ke fuskantar hukuncin kisa, sun kafa hujja ne da abkawa matar bisa zargin ta da yin yi mummunan shiga da ke fidda tsiraici.