Kenya: Masu bore sun sake fitowa a Nairobi
July 2, 2024Masu adawa da sabbin manufofin gwamnatin Kenya sun sake fantsama kan titunan Nairobi babban birnin kasar a ranar Talata 02.07.2024, sai dai jami'an tsaro da aka baza sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar da ke fadar ba dadi a game da tsadar rayuwa.
Karin bayani: Ci gaba da bore a Kenya duk da cewar gwamnati ta ci tuwon fashi
Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce zanga-zangar ta samu kauracewar kungiyar matasa ta 'Generation Z' duk da kiraye-kirayen hadakar kungiyoyin fararen fula masu yaki da tsadar rayuwa.
Karin bayani: Gomman masu zanga-zanga sun mutu a Kenya
Kawo yanzu dai wannan bore na adawa da sabon kasafin kudin kasar Kenya ya ritsa da rayukan mutane 31 a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch, sabanin adadin mutane 19 da shugaban kasar William Rutu ya bayar a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da yake sanar da janye sabuwa dokar.