1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kenya na jimamin mutuwar Raila Odinga

October 15, 2025

Madugun adawar Kenya Raila Odinga ya rassu a wannan Laraba a wani gari da ke kudancin Indiya yana da shekaru 80 a duniya.

Marigayi Raila Odinga, tsohon madugun adawar Kenya
Marigayi Raila Odinga, tsohon madugun adawar KenyaHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP

Shugaban Kenya William Ruto ya ayyana kwanaki bakwai na hutu domin jimamin mutuwar madugun adawan kasar Raila Odinga

Shugaba Ruto ya bayyana marigayin a matsayin 'daya daga cikin manyan masu kishin Kenya kuma babban jigo a Afirka wajen fafutikar kare dimokuradiyya da 'yanci, sannan kuma mutum da ba ya nuna gajiyawa wajen ganin an samar da jagoranci na gari'.

A cikin wannan makon guda na hutu da aka ayyana domin girmama gudummowar da Raila Odinga ya bayar ga kasar da ke gabashin Afirka, shugaba Ruto ya umurci a sassauto totocin Kenya a fadin kasar da kuma ofisoshin jakadancinta da ke kasashen ketare.

A lokacin da yake raye Raila Odinga ya yi zama dan majalisa na dogon lokaci, kafin ya rike mukamin firaminista daga 2008 zuwa 2013, sannan kuma ya tsaya takarar shugaban kasa sau biyar ba tare da mafarkinsa ya cika ba.