Kenya na juyayin 'ya'yanta da 'yan bindiga suka halaka
April 5, 2015Al'umar kasar Kenya, ta sadaukar da addu'o'in ta na Easter ga daliban Jami'ar Garissa 148 da mayakan Al Shabbab suka kashe a gabashin kasar a makon jiya.
Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar ya sha alawashin rama wannan kisar gilla da Al Shabbab ta aikata, ya kuma bukaci hadin kan al'umar a wannan loakci da kasar ke juyayi.
Kashe 80 cikin darin al'umar kasar Kenya dai mabiya addinin Krista ne.
Harin dai shi ne mafi muni da kasar ta fuskanta tun bayan harin Bom da aka kai kan ofishin jakadancin Amirka da ke Nairobi babban birnin kasar, a shekara ta 1998.
An kuma tabbatar da kama mutane biyar da ake zargin su da hannu cikin wannan hari, ciki kuwa har da wani dan kasar Tanzaniya Rasheed Charles, da aka same shi dauke da Gurnet, yayin da yake boye cikin rufin daki.