Kenya na shirin daukar sabbin jami'an kiwon lafiya
March 8, 2017Talla
A karo da dama gwamnatin ta Kenya ta sha yin barazanar korar wasu likitocin tare da kule wasu 'yan kwadago a gidan kurkuku domin tilasta musu da su koma bakin aikinsu.Ma'aikatan na kiwon lafiya na Kenya wadanda ke bukatar karin kudaden albashi na kuma bukatar a kara samar da kayayyakin aiki a cikin asibitocin na Kenya.