1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

William Ruto ya dare shugabancin Kenya

Ramatu Garba Baba LMJ
September 13, 2022

Mutane da dama sun jikkata a kasar Kenya, yayin turmutsitsin shiga filin wasan kwallon kafa da aka rantsar da sabon shugaban kasa William Ruto da ya dare kan madafun iko.

Kenya | Shugaban Kasa | William Ruto | Rantsuwa
Sabon shugaban kasar kenya, William Ruto yayin rantsuwar kama aikiHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Shi dai William Ruto ya kasance shugaban kasar Kenya na biyar da aka zaba a kan tafarkin dimukuradiyya, tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga Britaniya. Ruto ya yi alkwarin magance matsalolin cin hanci da rashawa da suka yi wa kasar katutu, tare da shawo kan rikicin kabilanci da ya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan kasar. Rahotannin sun nunar da cewa dubban jama'a ne suka cika filin wasan kwallon kafa na Moi da ke Nairobi fadar gwamnatin ksar, domin gane wa idanunsu yadda bikin ke wakana. Da yake rantsuwar kama aiki, Ruto ya mika godiyarsa ga mahalicci yana mai cewa ya tabbatar akwai Allah da yaa sanya shi da ya kasance ba kowa ba ya samu nasarar zama shugaban kasa.

Karin Bayani: Mata da dama sun samu mukamai a Kenya

Nan take kuma ya nada wanda ya gada, wanda kuma ya kasance tsohon shugaban kasar da ya yi wa mataimaki Uhuru Kenyatta ya ci gaba da jagorantar tattaunawar zaman lafiya a kasashen Habasha da Jamhuriyar Dimukuradiyar Kwango. Mai shekaru 55 a duniya, sabon shugaban kasar ta Kenya ya taba tallan kaji a gefen hanya kafin ya samu nasarar kasancewa fitaccen dan kasuwa a kasar. Ya dai yi takara da iyalan Raila Odinga da ke da karfi a siyasar kasar Kenya, wadanda suka yi uwa da makarbiya a siyasa tun bayan samun 'yancin kan kasar daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekara ta 1963. An haifi William Ruto a ranar 21 ga watan Disambar shekara ta 1966 a kauyen Sambut, shekaru uku ke nan bayan Kenya ta samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Dubban magoya baya, sun halarci bikin rantsar da sabon shugaban Kenya William RutoHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Ya yi karatunsa na firamare a makarantar firamare ta Kerotet  kana ya yi sakandare a makarantar Wareng kafin ya je babbar makarantar maza ta Kapsabet Boys. Daga Bisani ya halarci jami'ar Nairobi, inda ya yi digiri a fannin nazarin tsirrai da dabbobi ya kuma kammala a shekara ta 1990. Ya yi karatunsa na digirin digir-gir a jami'ar ta Nairobi, inda bayan tarin matsaloli ya samu nasarar kammalawa a shekara ta 2018. Ya yi nasarar haduwa da tsohon shugaban kasar Daniel Arap Moi yayin da yake jami'ar ta Nairobi, wanda kuma ya fara sanya shi a harkokin siyasa a yayin zaben shekara ta 1992. Ya kuma taba tsayawa takarar dan majalisar dokokin Kenya a shekara ta 1997, inda ya kasance dan majalisa daga shekara ta 1998 zuwa 2013. 

Karin Bayani: Raila Odinga zai kalubalanci sakamakon zabe a Kotu

Ruto ya rike mukamin ministan kula da harkokin cikin gida a shekara ta 2002, haka kuma ya rike ma'aikatar aikin gona daga shekara ta 2008 zuwa 2010. A shekarar ta 2010 dai, ya zamo misnitan kula da ilimi mai zurfi na kasar, kana ya kasance mataimakin shugaban kasar Uhuru Kenyatta daga shekara ta 2013 zuwa wannan shekara ta 2022 da muke ciki. Ya dai samu nasarar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Agustan da ya gabata, inda ya yi nasara kan abokin hamayyarsa Raila Odinga da tazara kalilan. Koda yake Odinga ya kalubalanci sakamakon zaben a gaban kotun kolin kasar, sai dai kotun ta tabbatar da nasarar Ruto. Da dama dai masu sanya idanu a yayin zaben, sun tabbatar da sahihancinsa. Sabon shugaban kasar ta Kenya William Ruto dai, na da mace daya da kuma yara bakwai. 

 


 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani