1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kenya ta sanar da makoki kan mutuwar hafsan kasar

April 19, 2024

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya sanar da zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar tun bayan mutuwar babban hafsan tsaron kasar Janar Francis Ogolla, sakamakon hadarin jirgin shelikwafta.

Hafsan tsaron Kenya marigayi Francis Ogolla
Hafsan tsaron Kenya marigayi Francis OgollaHoto: LUIS TATO/AFP/Getty Images

Shugaba Ruto ya sanar da zaman makoki ne domin nuna alhini da jimami kan mutuwar babban hafsan tsaron kasar Janar Francis Ogolla, sakamakon hadarin jirgi mai saukar Ungulu. 

Karin bayani: Masu zanga-zanga shida sun mutu a Kenya

Jirgin na dauke da mutane 11 ciki har da Janar Ogolla, inda ya yi hadari a wani yanki da ke kusa da iyakar kasar da Uganda, acewar shugaba William Ruto.

Karin bayani: Ambaliya ta kashe mutane 70 a Kenya

Hafsan tsaron kasar na kan hanyarsa ce ta zuwa yankin arewacin kasar da ke fama da rikicin 'yan bindiga. Har ya zuwa wannan lokaci babu tabbacin musabbabin afkuwar hadarin jirgin.