Kenya ta yi rashin ministan cikin gida
July 8, 2017Talla
Marigayin ministan dan shekaru 67 da haihuwa wanda tsohon janar na soja ne, ya mutu ne yayin da ake wata guda da zaben shugaban kasa a kasar ta Kenya.
Wani babban jami'i a fadar shugaba Uhuru Kenyyata, shi ne ya sanar da rasuwar babban jami'n a hukumance, yana mai kiran kasar ta yi juyayin rashi ba tare da la'akari da bambancin siyasa ba.
A daya hannun kuwa, rahotanni daga kasar na cewa wasu da ake zargin mayakan Al Shabaab ne, sun halaka mutane 9 a arewacin kasar. Maharan dai sun far wa wasu kauyuka biyu ne da ke yankin Lamu, inda bayanan mahukunta suka ce suni yi wa mutanen ne yankan rago.