1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya: Tsaurara dokar hana shan taba a wuraren jama'a

Staude, Linda / suleiman BabayoMay 31, 2016

A birnin Nairobi, an kebe wurare na musamman don shan taba, tare da tara mai yawa ga wadanda aka kama sun karya dokoki. Tuni lamarin ya fara samun martani daga mashaya taba.

Aschenbecher
Hoto: Colourbox/S. Chetanachan

A maimakon sayar da jaridu, da minti da kuma ruwan sha, runfa ce aka tanada domin masu shan taba sigari a bakin hanya. Louis wanda ya kasance daya daga cikinsu ya nuna rashin jin dadi:

"Wurin a cunkushe yake. Sau da yawa za ka ga mutane fiye da 100 a takure suna shan taba."

Wuraren da aka tanada domin shan taba sigarin sun kasance a lalace ba tare da kulawa ba. Kamar yadda Ben Sondego ya yi karin haske:

"Ba a kula da wuraren yadda ya kamata,, babu kyan gani, gwamnatin karamar hukuma ba ta kulawa yadda ya dace kamar yadda ake gani."

Wani mai shan taba shi ma ya nuna takaici kan yadda ake daukar masu shan taba sigari a kasar bada muhimmanci ba. A cewar wani mai shan tabar da ke da suna Louis dokar ta tana nuna musu tsangwama:

Hoto: Imago/teutopress

"Ba maganar zabi ba ce, kafin wannan lokaci mukan dan kewaya mu sha taba. Amma yanzu saboda dokokin da ka'idoji idan mutum bai yi hankali sai a kama shi ya shiga cikin fitina."

Dokokin na kasar ta Kenya sun kuma haramta shan taba sigari a cikin mota lokacin da mutum yake tare da yara kuma yake tuki. Louis ya kara da cewa yana ganin wannan ya zama kutse ga rayuwar mutane:

"Wannan ya zama shiga rayuwar mutane. Idan ka ce kar na sha taba a mota, ka shiga cikin rayuwa ta ke nan."

Akwai kimanin 'yan Kenya milyan uku da ke shan taba sigari. Abin da ke zama adadi mai yawa cikin kasashen kudu da Sahara na Afirka. Kepha Ombachi shi neke zama daraktan kula da lafiyar al'umma ta kasar ta Kenya, wanda ya kare dokokin:

"Muna nuna damuwa kan kare lafiyar al'ummar Kenya, da mutanen da suke rayuwa a Kenya kan abin da za mu iya karewa."

Gonar ganyen yin taba sigariHoto: picture-alliance/Chad Ehlers

Da wannan tara mai yawa, idan aka kama wanda yake shan taba sigari a bainan jama'a zai iya fuskantar dauri na tsawon watanni shida ko kuma tara ta kimanin kudaden Euro dubu-biyar. Ga mashaya taba wannan ba abu ba ne da zai hana komai. Kamar yadda Ben Sondego ke cewa:

"Babu yadda za ace idan aka saka dokokin takaita shan taba mutane za su daina, haka ba zai kasance ba. Abu ne na tunani, da rayuwa da kuma tattalin arziki gami da al'ada. Sai an koma wannan wuraren idan muna son taimakon mutane daina shan taba sigari."

Bayan da babbar kotun kasar ta Kenya ta yi watsi da karar da babban kamfanin taba sigari ya shigar, yanzu babu abin da ya rage sai dai masu shan taba su yi amfani da wuraren da aka kebe musu domin shan taba sigarin.