1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

Wanene jagoran adawar Kenya da ya rasu?

October 15, 2025

Tsohon jagoran adawar Kenya, Raila Amolo Odinga da ake ganin shi ne kusa a adawar siyasar kasar sama da shekaru 30 ya rasu yana da shekaru 80 a duniya.

Kenya | Nairobi | Rasuwa | Jagoran Adawa | Raila Amolo Odinga
Jagoran adawar kasar Kenya Raila Amolo Odinga da ya kwanta damaHoto: Simon Maina/AFP

Ana iya tunawa da Raila Amolo Odinga a matsayin mutumin da ya yi rawar gani, a tafiyar dimukuradiyyar kasar Kenya. Jaridar Associated Press ta ce Odinga ya rasu ne sakamakon bugun zuciya a Kerala, inda yake jinya a asibitin Devamatha. Kamar yadda shi ma kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa Odinga ya rasu ne yayin duba lafiyarsa.

Jami'an 'yan sandan Indiya sun bayyana cewa Odinga ya fadi ne kwatsam, yayin da yake tafiya tare da 'yar uwarsa da diyarsa da likitansa. A tsawon shekaru da dama Odinga ya kasance fitaccen dan adawa a Kenya da ya yi fafutukar ganin an samu dimukuradiyya ta jam'iyyu da dama, kana mutum ne da ke kalubalantar mulkin kama-karya da neman zaman lafiya a lokutan rikicin siyasa.

Rayuwarsa

Raila Amolo Odinga a yayin gangamin yakin neman zabensa a shekara ta 1997Hoto: Alexander Joe/AFP

An haifi Raila Odinga ne a ranar bakwai ga watan Janairun 1945, a garin Maseno da ke lardin Kisumu a yammacin Kenya. Mahaifinsa Jaramogi Oginga Odinga shi ne mataimakin shugaban kasa na farko, bayan samun 'yancin kan kasar. Raila ya yi karatu a Kisumu Union Primary da Maranda High School kafin ya sami gurbin karatu a Tarayyar Jamus ta Gabas a shekarar 1965, inda ya kammala digiri a fannin injiniyan masana'antu a 1970.

Bayan ya koma gida ya koyar a jami'ar Nairobi, sannan ya yi aiki a Hukumar Kula da Ma'aunin Kayayyaki ta Kenya. Daga nan ya kafa kamfanin masana'antu na East African Spectre, wanda ke sarrafa tankokin iskar gas. Odinga ya shiga siyasa dumu-dumu ne a lokacin mulkin jam'iyyar KANU mai kama-karya a shekarun 1980, inda aka yi ta tsare shi saboda fafutukar da yake yi ta ganin an kafa jam'iyyu da dama.

Al'ummar Kenya na jimamin rasuwar jagoran adawar kasar Raila Amolo OdingaHoto: Thelma Mwadzaya/DW

A 1992 aka zabe shi dan majalisa na mazabar Langata, zaben da ya bude masa kofar siyasa a matakin kasa. Ya tsaya takarar shugaban kasa a 1997, inda ya zo na uku bayan Daniel Arap Moi da Mwai Kibaki. Daga bisani ya kafa jam'iyyar NDP, sannan ya hada karfi da sauran jam'iyyun adawa wajen kafa jam'iyyar National Rainbow Coalition (NARC) da ta kawo Kibaki kan karagar mulki a 2002.

Karin Bayani: Zanga-zangar 'Yan adawa a Kenya

Daga shekara ta 2003 zuwa 2005 Raila Odinga ya rike mukamin ministan ayyuka da gidaje, kafin rikici ya barke tsakaninsa da Kibaki ya koma adawa. A 2007 ne marigayi Raila Odinga ya shiga babban rikicin siyasa, bayan da Hukumar Zabe ta ayyana Kibaki a matsayin wanda ya lashe zabe duk da cewa alamu sun nuna shi Odingan ne ya fi samun goyon bayan jama'a.

Shin shugaban addinin Kirista na Kenya ya yi laifin kisa?

01:24

This browser does not support the video element.

Rikicin bayan zabe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 1,000, yayin da dubbai suka rasa matsugunansu. Bayan tattaunawa karkashin jagorancin tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan an cimma yarjejeniyar raba iko, inda Raila Odinga ya zama Firaminista daga 2008 zuwa 2013.

Mutum mai tasiri da bai zama shugaban kasa ba

Sai dai duk da wannan matsayi ya ci gaba da kasancewa jagoran adawa, inda ya sake tsayawa takara a shekarun 2013 da 2017 da 2022 amma bai taba samun nasarar zama shugaban kasa ba. A 2025, shugaban kasa William Ruto ya nada shi wakilin musamman don sasanta rikicin Kudancin Sudan, wata alama ta girmamawa daga abokan hamayya.

A 2024 kuma Raila ya nemi mukamin Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka (AU), amma ya sha kaye a hannun dan kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf. Marigayin dan siyasar Raila Odinga dai, ya bar tarihi mai zurfi a siyasar Kenya. Wanda bai taba zama shugaban kasa ba, amma ya taimaka wajen tabbatar da 'yancin dimukuradiyya da yawancin al'ummar Kenya ke cin amfaninsa a yanzu.