Kenya: 'Yan adawa sun soma zanga-zanga
August 9, 2017Birnin na Kisumu dai na a matsayin daya daga cikin manyan biranen kasar ta kenya inda dan adawan ke da tarin magoya baya. Daruruwan mutane ne suka fito a wata unguwa ta birnin tare da kafa shingaye da kuma kona tayoyi don nuna adawa da sakamakon zaben. Sai dai masu sa ido na tarayyar Afirka ta bakin shugaban tawagar tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki, zaben ya gudana yadda ake so:
Hukumar zaben kasar Kenya ta yi abin azo a gani wajen shirya zabe mai kyau, kuma jama'a sun fito sun yi dafifi. Ana iya cewa hukumar ta cika burinta domin ta aike da wakilanta a ko'ina, don haka a matsayina na dan Adam dan Afirka, ina iya cewa na yi farin ciki da abun da muka gani a zaben Kenya.
Sai dai masu zanga-zangar na birnin Kisumu sun tsaya kan bakansu na cewa Shugaba Uhuru Kenyatta ba shi ne ya lashe wannan zaben ba, kuma idan har Raila Odinga bai zama shugaban kasa ba to babu sauran zaman lafiya a cewar su.