Kenya za ta gudanar da bincike akan hatsarin jirgin sama da ya auku
June 10, 2012Talla
Fraministan ƙasar Kenya Raila Odinga ya ce za a gudanar da bincikke mai zurfi bayan aukuwar hatsarin jirgin saman ;wanda a ciki ministan tsaron na kasar George Saitoti ya rasa ran sa tare da wasu muƙaraban sa.Mista Saitoti wanda aka shirya zai tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar nan gaba , na daga cikin ƙusoshin gwamntin da ke yaƙi da ta'adanci a ƙasar Somaliya.
jirgin saman mai saukar ungula wanda ke ɗauke da mutane biyar ya tarwatse NE a tsaunin Kibiku kusa da birnin Nairobi inda minista zai halarci wani taro.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala