Kenya za ta janye daga kotun ICC
September 5, 2013Talla
Tun da farko a yau a ƙasar Hollande da ta ke yin magana Babbar alƙalin kotun Fatou Bensuda ta ce kotun ta ICC za ta ci gaba da shirin gurfanar da shugabanin ƙasar wato shugaban ƙasar Nhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto.
Dangane da zargin samun su da hanu a cikin tashin hankali da ya biyo bayan zaɓuɓɓukan shekarun 2007, wanda a ciki mutane dubu daya da ɗari biyu suka rasa rayukansu. An dai shirya yin shari'a ta Ruto a cikin watan Satumba kafin a yi ta Nhuru Kenyatta a ranar 12 ga watan Nuwamba da ke tafe.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu