Kenyata ya zargi Kotu da yin juyin mulki
September 21, 2017Talla
Kenyata ya yi wadannan kalamai ne a yayin da ya ke tsokaci a gidan talabijin na kasar, bayan da kotu ta sanar da matsayanta kan hujjojin soke zaben. Shugaban ya ce 'yann adawa sun yi amfani da kotun wajen yin juyin mulki.
Hukuncin kotun na ranar 1 ga watan Satumba shekara ta 2017, shi ke zama hukuncin kotu na farako da ya yi tasiri wajen rusa zaben shugaban kasa a nahiyar Afirka. A yanzu dai a ranar 17 ga Oktoban da ke tafe ne kotun kolin kasar ta Kenya ta bada umarnin sake shirya sabon zaben shugaban kasar.