Kenyatta zai gana da Trump
August 27, 2018Talla
Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya zai gana da shugaban Amirka Donald Trump a wannan Litinin, watanni kalilan da fitar da Kenyar ta yi daga rikicin siyasa.
Shugaban Kenyatta dai shi ne shugaban kasar bakar fata na biyu da zai gana da shugaban na Amirka, bayan Shugaba Buhari na Najeriya.
Ofishin shugaban kasa a Kenya, ya ce shugabannin biyu za su maida hankali ne kan harkokin cinikayya da kuma na tsaron yankin gabashin Afirka.
Kasar ce ta uku da ke samun taimako ta fuskar tsaro daga Amirka, cikin kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara.
Kasashen biyu kuwa na da dakarunsu a kasar Somaliya inda mayakan al-Shabaab ke gwagwarmaya da makamai a yankin.
A halin yanzu dai kasar China ce ke kan gaba wajen mamaye kasuwannin nahiyar Afirka.