1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman cirewa Sudan takunkumi

Zainab Mohammed Abubakar
August 25, 2020

A rangadin aikin da ya kai a birnin Khartoum, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya tattauna muhimman batutuwa da suka dangtanci dangantaka da mahukuntan kasar Sudan.

Abdalla Hamdok
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Fraministan Sudan Abdallah Hamdok ya sanar da ganawar keke da keke kan muhimman batutuwa da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo a birnin Khartoum, ciki har da batun cire Sudan a jerin kasashen da Washington ta ayyana a daukar nauyin 'yan ta'adda. 

Pompeo ya isa Kartoum ne daga Izra'ila, a kokarin Amurkan na karfafa dangantaka tsakanin Sudan da Izra'ila.

Ziyarar tasa na bangaren rangadin yankin ne, bayan cimma yarjejeniyar maido da dangantaka tsakanin kasar ta Baniyadu da Hadaddiyar Daular Larabawa cikin wannan wata.

Amurkan dai na neman sauran kasashen Larabawa da su bi sawun Abu Dhabi. Tun a zamanin mulkin hambararren shugaba Omar Hassan al-Bashir nedai, Washington ta kakaba wa Sudan takunkumi saboda zarginta da goyon bayan kungiyoyin tarzoma da kuma yakin batsatsan lardin Darfur.