Khashoggi: Saudiyya ta gargadi kasashe
February 8, 2019Talla
Adel al-Jubeir da ke zaman karamin ministan harkokin wajen Saudiyya din ya ce duk wani mataki da za a dauka kan Muhammad bin Salman game da kisan na Khashoggi daidai ya ke da takalar kasar da fada wanda in an san farkonsa ba a san karshensa ba.
Ministan ya ambata hakan ne yau lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a birnin Washington na Amirka, inda galibin 'yan majalisar dokokin kasar ke cewar Yarima Bin Salman din ne ke hannu wajen kisan Jamal Khashoggi, batun Saudiyya din ke cewar zargi ne da bai da tushe balle makama.