1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birnin Kherson ya koma hannun Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou
November 12, 2022

Sojojin Ukraine na cigaba da sintiri don tabbatar da doka da oda a wasu sassan birnin Kherson bayan da Rasha ta kammala janyewa daga yankin.

Ukraine, Kiew | Freude darüber das Cherson wieder unter ukrainischer Kontrolle ist
'Yan Ukraine na murnar karbe iko da birnin Kherson Hoto: Genya Savilov/AFP/Getty Images

Wasu kasashe aminan Ukraine na cigaba da aika sakon taya kasar murnar karbe iko da yankin Kherson na kudancin kasar daga Rasha, makwanni bayan da ta ayyana shi a daya daga cikin yankunanta.

Amirka ta bayyana nasarar a matsayin gagaruma a yayin da Faransa ta ce ta yi farin cikin ganin yankin ya koma karkashin Ukraine.

Shugaba Zelensky, ya bayyana nasarar a matsayin irinta ta tarihi da sojojin kasar suka yi, tare da cewa yanzu sojan kasar ne ke sintirin don tabbatar da doka da oda.

A sakon da ya bayyana a wannan Asabar ministan harkokin wajen Uklraine Dmytro Kouleba, ya ce za a ci gaba da fafatawa sannan kasar na da bukatar ci gaba da samun tallafin aminanta.