Mabiya cocin Kibdawan bakwai sun mutu a harin 'yan bindiga
November 2, 2018Talla
Rahotannin na cewa, akwai mutane akalla bakwai da suka jikkata a sanadiyar harin. Tuni dai aka kaddamar da bincike da kuma farautar wadanda ke da hannu a harin. An kai harin kusa da wurin da aka kai wani hari makamancin na wannan rana a watan Mayu na shekarar 2017 da ya halaka Kibdawa ashirin da takwas.
Shugaban Masar Abdelfatah al-Sisi, a wani sakonsa bayan harin, ya jajantawa iyalan mamatan inda ya kuma sha alwashin ci gaba da yakar 'yan bindaga da suka buwayi kasar da ayyukan ta'addanci.