1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mawaka na waken yaki da Coronavirus

March 31, 2020

Yayin da adadin mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus ke karuwa tare da samun asarar rayuka, lamarin da ke sa fargaba ga al'umma, makada da mawakan zamani sun raja'a ga fitar da wakokin wayar kai dangane da cutar. 

Trommler im Studio
Hoto: Colourbox

Wasu mawakan zamani na rere wakokin a shafukan sada zumunta da kafofin yada labarai. Ali Atchibilli shi ne manajan mawakan "Haske Star", da ya fitar da wakar. Irin wanan gudunmawa ta wayar da kan jama'a da zaran irin haka ta samu, nauyi ne da ya rataya a kan kowacce kungiya.

To amma ga Mahaman Mutari Eldezire dan jaridar da ke bibiyar shafukan sada zumunta ko journaliste en ligne dole sakon ya kai ga jama'a. Irin wadannan wakokin wayar da kan jama'ar dai sun mamaye zukatan al'umma, musamamn matasa da ke bibiyar shafukkan sada zumunta