1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kidayyar kuri'u ta kankama a sassan Najeriya

February 25, 2023

Bayan share tsawon lokaci suna bin layi don kada kuri'a, miliyoyin 'yan zabe na tarrayar Najeriya sun fara jiran sakamakon zaben da ke zaman mafi daukar hankali a shekarun baya-bayan nan.

Yadda zabe da kidaya ke gudana a wata rumfar zabe a NajeriyaHoto: SAMUEL ALABI/AFP/Getty Images

An tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na majalisun tarrayar a cikin wata rumfar zabe a unguwar Gwarimpa da ke Abuja da sauran sassa na Najeriya. Amma an rufe rumfunan zaben Abuja ba tare da rahoton cinikin kuri'ar da ke zaman al'ada a fagen siyasa ba. Ana kallon zaben a matsayin mafi rashin tabbaci cikin tarihin zabe a kasar,  inda da kamar wuya a kai ga hasashen mutumin da ke shirin gadon Shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan dai shi ne karo na farko a shekaru 20 da doriya da 'yan kasar ke zaben da babu tsohon soja cikin manyan masu takara ta shugaban kasar guda hudu. A wani abu da ke nuna alamun karshe na babakeren sojojin da suka share lokaci cikin kayan sarki, sannan suka rikide da daukar kasar da sunan farin kaya.

Na'urar Bvas ta taka muhimmiyar rawa a zaben NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Ita kanta sabuwar na'urar BVAS da ke tantance 'yan zaben ta fasaha ta zamani ya burge masu zaben na bana a fadar Jummai Mana da ke zaman daya a cikin masu zabe. Kasimu Mohammed da ya share shekaru 45 yana taka rawa a zabe, ya ce batun kudi ya narke a rumfunan yin zabe.

Hukumar EFCC ta masu yaki da cin hanci ta rika zagayawa rumfunan zabe da nufin farautar dillallan kuri'a a cikin garin  Abuja.  Abdurasheed Bawa da ke zaman shugaban hukumar na kasa ya ce sun yi nasarar hana amfani da kudi da nufin sauya ra'ayin masu zabe.  A yayin da jami'an tsaron suke fadin sun hana cinikin kuri'a, shi kansa shugaban kasar da ke shirin barin gadon ya ce dillacin kuri'ar ya zama tsohuwar sana'a a kasar.

Shugaba EFCC Abdurasheed BawaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

A ranar lahadi ne dai ake saran fara samun sakamakon majalisun tarrayar kasar 469, kafin kila a samu na shi kansa shugaban kasar ya zuwa farkon makon da ke tafe.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani