Kifewar kwale-kwale ta halaka mutane sama da 60 a Najeriya
September 15, 2024Ana fargabar mutuwar mutane 64 bayan kifewar kwale-kwalen da suke ciki ranar Asabar a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamafaran Najeriya, kasancewar mutane 6 kacal aka samu damar cetowa daga cikin 70 din da suka dulmiye a cikin ruwan.
Karin bayani:Zamfara: Mutane da dama sun nutse a ruwa
Shugaban karamar hukumar ta Gummi Aminu Nuhu Falale, ya ce kwale-kwalen na dauke da manoma 70, a kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu da safiyar Asabar, to amma ma'aikatan agaji sun samu nasarar zakulo 6 a raye, sannan kuma suna ci gaba laluben sauran wadanda suka nutse a cikin ruwan.
Karin bayani:Matsalar tsaro ta sa jama'a barin garuruwansu a Zamfara
Kimanin kusan manoma dubu daya ne ke jigilar zuwa gonakinsu ta wannan yanki a kullum rana, to amma kwale-kwalen ruwa guda biyu ne kacal suke amfani da su domin wannan zirga-zirga, lamarin da ke janyo cikar jiragen ruwan fiye da kima a duk lokacin da suke tafiyar, kamar yadda wani mai rike da sarautar gargajiya na yankin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.