SiyasaKoriya ta Arewa
Kim Jong Un ya nada 'yarsa mai jiran gado
February 12, 2026
Talla
Kim Ju Ae 'yar kimanin shekara 13 da haihuwa ta baiyana daura da mahaifinta a tarukan soji.
Wani dan majalisar dokokin Koriya ta Kudu Lee Seong-Kweun ya wallafa bayanan tattaunawar sirri da hukumar leken asirin Seoul.
A baya dai hukumar leken asirin ta baiyana Kim Ju Ae wadda ke karatu a matsayin mai jiran gado amma a yau kalaman da aka yi amfani dasu sun ce ana dab da nada ta mai jiran kujerar mulki kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Lee ya ce hukumar leken asirin ta kasa ta yi la'akari da abubuwa da dama ciki har da baiyanar da ta ke yi a tarukan gwamnati a hukumance.