1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

111010 Primor Nahost

October 12, 2010

Farin jinin Isra'ila na raguwa a idanun duniya, sakamakon matakan da take ɗauka na yin gaban kanta.

Benjamin Netanyahu Firai ministan Isra'ilaHoto: AP

Batun Isra'ila da Palasinawa dai yanzu ya sake dawowa kafafen yaɗa labarai, bayan da tattaunawar da aka fara wata guda ta ruguje, sakamakon ci gaba da gina matsugunen Yahudawa a yankunan Larabawa. Yanzu haka dai dangantakar Isra'ila da ƙasashen Turai sannu a hankali ta fara yin tsami musamman bayan ministan harkokin wajen Isra'ila ya yi kalamen ranen wayo ga ministocin EU da suka ziyarci ƙasar. Usman Shehu Usman na ɗauke da ci gaban labari.

Yanzu dai lokaci ne da gwamnatin Isra'ila ke fiskantar matsala kan yadda za ta jawo hankalin ƙasashen duniya su martaba ta, kamar yadda Avi Primor tsohon jakadan Isra'ila a ƙasar Jamus ke cewa. Duk da shekaru sha ɗaya da ya yi da komawa a ƙasarsa bayan aikin dipalmasiya, har yanzu mai ana jin muryarsa a kafafen yaɗa labarai, kuma a duk lokacin da aka tambaye shi kan batun zaman lafiya yana mai nuna cewa abun baya tafiya yadda yakamata, domin Isra'ila tana ƙara zama saniyar ware a al'amuran ƙasa da ƙasa.

Haka dai lamura ke ƙara taɓarɓarewa ga Isra'ila, a ƙasar Jamus lamarain bai kai wasu wuraren ba, amma dai mutuncin ƙasar sai ƙara zubewa yake yi a duniya. Ƙasarmu ƙaramar ƙasace, 'yar mitsitsiya, Kuma ba za mu iya yaƙar duniya baki ɗaya ba. A kwai mutane da yawa a ƙasar Isra'ila da suka fahimci hakan, zan iya cewa su suka fi yawa, amma abun kaito har yanzu bamu ko yi darasi ba"

Avi Primor tsohon jakadan Isra'ila a JamusHoto: dpa - Fotoreport

Ita ma kanta gwamnatin Isra'ila ba ta farga cewa mutuncin ta na ƙara zubewa ba, domin da ta yi la'akari da hakan da ba ta koma ga gina matsugunan yahudawa ba, duk da kiran da ƙasashen duniya suka yi mata na dakatar da shirin, wanda hakan ya katse tattaunawar zaman lafiya da aka fara. Kamar yadda Avi Primor ke cewa, ƙasar Amirka ce kawai za ta iya sake dawo da ɓangarorin biyu su koma tattaunawar da suka fara.

"Amirka ta matsa musu lamba da su tattauna ababen da suka fi kawo tarnaƙi zakaninsu, bawai ga batun gina matsugunan Yahudawa kawai ba, duk da cewa wannan shima yana da mahimmanci. Yakamata su mai da hankali kan makomar kafa ƙasar Palasdinu mai 'yancin kai"

Ga jami'in dipalmasiyan na Isra'ila mai kushe manufar ƙasarsa, yace ana ɓata lokacine kawai, a ja in ja kan matsugunai, amma da kamata ya yi a tattauna batun kan iyakar ƙasar Palasɗinu da za'a kafa, a son inane iyakar Isra'ila, idan da an yi haka to da an rufe batun 'yan share wure zauna.

Matsugunan Yahudawa a yankunan LarabawaHoto: AP

"Idan da Isra'ila ta amince da iyakar da aka shatawa Palasɗinawa wanda kuma duniya ta yar da da ita, to da ai su kansu 'yan share wuri ka sauna, ba su samu damar tsallaka yankunan Palasɗinawa ba. Domin sai dai su yi borenda za su yi, amma dole su yi zaɓi kodai su kasance cikin ƙasar Palasɗinu ko su dawo cikin iyakar Isra'ila. Kuma sanin kowa ba za su zaɓi zama cikin ƙasar Palasɗinu ba, hakan bai dace da manufar su ba"

Avi Primor yace idan aka dubi ƙungiyar Hamas dake iko da zirin Gaza, to lallai Isra'ila na buƙatarsu shiryawa da su, domin idan bata shirya da Hamas ba to kuwa babu zaman lafiya a agreta, haka a gefe guda, ita ma Hamas tana buƙatar a samar da zaman lafiya, domin in ba haka ba za ta rasa goyon bayan da Palasɗinawa ke basu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman da Bittina Max.

Edita: Abdullahi Tanko Bala