1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Daraktar hukumar leken asirin Amurka ta yi murabus

Abdourahamane Hassane
July 24, 2024

Darakatar hukumar ta yi marabus a daidai lokacin da Kamala Haris za ta soma yin yakin neman zaben na farko a Jihar Wisconsin, jiha mai mahimmanci a gareta a fafatawar da za ta yi da Donald Trump.

Kimberly Cheatle
Kimberly Cheatle Hoto: Kevin Mohatt/REUTERS

 Kamala Haris yar shekaru 59 wadda aka yi hasashen cewar tana da amanar delegate sama da dubu biyu  wajen zabenta domin ta gaji Biden, don tabbatar da ita,tana da kasa da watannin hudu na shawo kan al'umma a yakin neman zaben. Joe Biden, wanda yake murmurewa daga cutar Covid, zai koma Fadar White House, bayan killaceshi da aka yi, kusan mako guda a gidansa na hutu a Rehoboth, a gabar Tekun Atlantika.Halin da ake ciki kuma daraktar hukumar leken asirin Amirka Kimberly ta yi marabus saboda yawan sukar da ake yi mata kan gazawa wajen kare Donald Trump daga harin dan bindiga, wacce ta amsa laifin  gazawar.