Kin mutunta takunkumi Koriya ta Arewa
September 21, 2017Kasashen na Afirka dai na ba da muhimmanci ga kyawawan dangantaku da ke tsakaninsu da Koriya ta Arewar tun a zamanin yakin cacar baka. A kasashen Afirka da dama akwai mutum mutumi na tagulla na mashahuran shugabanni da masana'antar kera mutum mutumi na kasar Koriya ta Arewa wato Mansudae Overseas Project ta yi. Kamfanin na gwamnati ya kwashe shekaru gommai ya na gina sansanonin soji a kasashen ketare wanda hakan ke samar wa shugabannin Koriya ta Arewa makudan kudade.
A kasar Namibiya ga misali, kamfani ya yi aikin manyan gine-gine guda hudu ciki har da na sabuwar fadar shugaban kasa a birnin Windhuk a shekarar 2008. Baya ga haka Majlisar Dinkin Duniya ta ce daga shekarar 2002 Namibiya ta kashe sama da dalar Amirka miliyan 100 a wasu aikace-aikace na iyalin gidan Kim ciki har da masana'antar albarusai. A saboda haka ake zargin kasar da karya ka'idojin takunkuman Majalisar Dinkin Duniya kan Koriya ta Arewa
Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa awaki kasashen kimanin 10 da ke karya ka'idojin takunkuman da suka fara aiki kan Koriya ta Arewa tun shekarar 2006 kuma yanzu haka ana gudanar da bincike kansu amma masana sun ce yawan kasashen na Afirka da ke da huldar kasuwanci ba bisa ka'ida ba da gwamnatin Pyongyang sun haura wanda aka sani kamar yadda masanin nan na cibiyar Chatham House Daragh Neville ya shaida inda ya ke cewa "ko da ya ke a jimilce kudin kasuwanci na kimanin dala miliyan 100 babu yawa amma ga Koriya ta Arewa kudi ne mai yawa daga ketare domin ya na da wahala ga gwamnati ta samu kudin musaya na ketare. Ga kasashen Afirka kuwa yana da araha su yi kasuwanci da Koriya ta Arewa domin sabanin abokan huldarsu na kasashen yamma ita ba ta yi musu shisshigi."