Kira ga daukan matakai kan tsaron Libiya
December 11, 2014Wakiliyar ta Majalisar Dinkin Duniya Hiroute Guebre Sellassie ta tunatar da yadda aka fuskanci kwararar makammai zuwa sassa daban-daban na yankin Sahel, tare da bunkasar safarar muyagun kwayoyi tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Mouammar Kadhafi a shekarar 2011, inda a yanzu kasar ke karkashin jagorancin gwamnatoci biyu da kowanne ke ikirarin cewa shi ne jagora na gaskiya.
Wakiliyar ta kara da cewa a kalla an shigar da makammai dubu 20 zuwa yankin Sahel daga Libiya, kuma mafi yawan muyagun kwayoyi da ake safara, na bi ne ta yankin na Sahel.Tuni dai dama ake rade-radin cewa kungiyar 'yan jihadi ta IS ta girka sansanoni na foras da mutanen ta a kasar ta Libiya, abun da ke kara tayar da hankulla a cewar ta.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba