Kira ga Rasha kan hadin kan Ukraine
November 3, 2014Wannan kira yazo ne bayan da 'yan awaren gabashin kasar ta Ukraine suka zabi shugabanninsu a zabubukan da suka gudanar na shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a jiya Lahadi. Shugaban diflomasiyar kasar ta Jamus ya ce wannan zabe da ke matsayin jeka-nayi-ka a idanun kasashen Turai, zai iya kawo cikas ga yarjejeniyar da aka cimma a birnin Minsk tsakanin hukumomin na Kiev da na Moscow a ranar biyar ga watan Satumbar da ya gabata. A nata bangaren Rasha ta yi kira ga hukumomin Ukraine da su daina daukar duk wani mataki na soja a yankin gabashin kasar, inda ta ce sababbin hukumomin da aka zaba a wadannan yankuna na da hurumin tattaunawa da hukumomin na Kiev dan samun kwanciyar hankali mai dorewa.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Umaru Aliyu