1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiristocin ƙasashen Larabawa na fiskantar barazana

Usman ShehuOctober 30, 2013

Rikicin da ke faru a Gabas Ta Tsakiya ya saka Kiristocin yankin a wani halin fargaba da rashin tabbas, inda ake ta kai musu hare-hare

Pope Tawadros II (C), the 118th Pope of the Coptic Orthodox Church of Alexandria and Patriarch of the See of St. Mark, leads the Coptic Christmas Eve Mass at St. Mark Cathedral, in Cairo January 6, 2013. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany (EGYPT - Tags: RELIGION ANNIVERSARY)
Bikin Ƙiɗawan MasarHoto: Reuters

Boren neman sauyi da a yanzu haka ke ci gaba da faruwa a ƙasashen Larabawa, ya haddasa barazana ga rayuwar Kiristoci da ke yankin. Tashe-tashen hankula na siyasa da suke faruwa a yankin, suna ƙarawa ƙungiyoyi masu kaifin kishin addinin Islama ƙarfi, yayin da su kuwa Kiristoci wasunsu ke tserewa daga ƙasashensu na asali. Bisa waɗannan dalilan ya sa majalisar Kiristoci a yankin ta ke son nunawa 'yan uwansu dama duniya, irin wannan matsalar da suka samu kansu.

A cikin shekaru ukun da suka gabata dai, Kiristoci da dama a yankin Gabas Ta Tsakiya suka shiga wannan yanayi mawuyaci a rayuwarsu, sakamakon guguwar neman sauyi da ta kaɗa a yankin. Habib Badr, shi ne Father da ke kula da Mujami'ar Evangelika da ke a birnin Beirut na Lebanon, wanda a yanzu yake cikin babbar damuwa, kan halin da Kiristoci suka shiga a yankin.

Wata mujami'a da aka ƙona a MasarHoto: AFP/Getty Images

"Guguwar neman sauyin ta baiwa ƙungiyoyi masu kaifin kishin Islama ƙarfi. Lamarin ya sauya tinanin kowa, walau Musulmi ko Kirista da dai sauransu. Idan dai suka ƙi ba da hadin kai, imma dai a ci zarafinsu ko kuma a hallaka su. A nan mu kiristoci a Gabas Ta Tsakiya tsiraru ne, don haka mu aka fi gallazawa. A yanzu muna tserewa daga ƙasashenmu na asali"

Dama can dai Kiristocin sun hangi irin wannan matsalar tun fara bore a yankin. Don haka ne ma a bara suka kafa wata majalisa da suka kira (Assambly of Eastern Christians) inda suke taruwa don tattauna matsalolinsu, kana su kan karɓi rahotanni daga sassan, domin jin halinda ake ciki. Fuad Abu Nader, mamba ne a majalisar daga ƙasar Lebanon.

Kiristocin SiriyaHoto: picture-alliance/dpa

Ya ce "Muna son mu hada kai, mu kuma nuna addinin da muke bi na Kirista. Ganin yanayin da aka shiga a Gabas Ta Tsakiya, bai kamata mu tsaya muna magana kan mujami'ar da mutum yake bi. Don haka so muke mu riga magana da murya guda"

Wannan majalisar Kiristocin dai an kafa ta ne tun a tsakiyar shekarun 1970, amma saboda matsalar cikin gida da ta fuskanta, majalisar ba ta yi wani tasiri ba. Sai dai a yanzu ganin halin da aka shiga a yankin, Abu Nader ya ce, ya zama wajibi su nemi wata murya guda da za ta kare muradunsu. Shi kuwa Habib Badr, ya ce akwai buƙatar majalisar ta nemi hadin kai da Musulmai.

Mujami'a da Masallaci a haɗe a SiriyaHoto: picture-alliance/dpa

"Dole ne mu haɗa kai da Musulmai, domin su shawo kan masu tsattsauran ra'ayi da ke cikinsu. Domin su ma suna daga cikin wadanda wannan lamarin ya shafa. Don haka ya zama wajibi a buɗe wata ƙofar tattaunawa da 'yan Sunni, waɗanda su ne suka fi yawa a yankin"

A Gabas Ta Tsakiya dai an yi kiyasin cewa Kiristoci sun kai kashi 10 cikin ɗari na al'ummar yankin. Kiristocin da suka fi yin fice su ne Ƙibɗawa a ƙasar Masar, sai kuma na Siriya ke bi a baya. A ƙasar Lebanon akwai Kiristoci da dama da ke riƙe da muƙaman gwamnati. A ƙasar Masar kimanin mujami'u 43 da gidajen Krisitoci 200, masu kaifin kishin addini suka kai wa hari, tun fara tarzumar siyasa a ƙasar. Yanzu haka a ƙasar Iraƙi bai fi ɗaya bisa biyar na Kiristocin ƙasar ke zama a ciki ba, inda suka tsere sakamkon hare-haren da ake kai musu, tun bayan kifar da gwamnatin Marigayi Saddam Hussein a shekara ta 2003.


Mawallafa: Mona Naggar / Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu