SiyasaTurai
Kirsimeti 2021: Paparoma na son a mutunta dan Adam
December 25, 2021Talla
Shugaban mabiya darikar katolika ta duniya Paparoma Francis ya yi kira ga mabiyansa da su gode wa kalilan da Allah ya huwace musu a rayuwa. A jawabinsa na jajibirin Kirsimeti na bana, Paparoma ya ce Kirstocin da ke kuntata wa talaka na yin mummunan sabo.
Paparoman ya yi bayani a kan darajar dan Adam, inda ya ce Ubangiji yana tunasar da mabiya muhimmancin kula da hakkin ma'aikata maza da mata. Ya ce ya kamata a kawo karshen mutuwar da wasu ke yi a wuraren ayyukansu.
Dokokin corona sun rage kusan sau biyar na adadin mutanen da ke halartar jawabin na shekara-shekara. Sai dai wadanda ba su zo wurin ba sun kalli jawabin kai tsaye ta hanyar bidiyo daga gidajensu.