1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kirsimeti: Steinmeier ya bukaci zaman lumana a duniya

December 24, 2023

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya bukaci a samar da hadin kai a ciki da wajen kasar don tunkarar kalubalen da kasar da kuma duniya ke fuskanta.

Hoto: Britta Pedersen/dpa/picture alliance

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya bukaci a samar da hadin kai a ciki da wajen kasar don tunkarar kalubalen da kasar  da kuma duniya ke fuskanta. Wannan na daga cikin rubutaccen jawabin shugaban wanda ofishinsa ya fitar a jajibirin Kirsimeti da ake sa ran zai gabatar wa 'yan kasar a gobe Litinin.

Shugaban ya ce wannan shekarar na tattare da manya-manyan kalubale; kama daga yakin Rasha da Ukraine da aka shiga shekara ta biyu, da kuma yakin da Hamas ta takalo a Gabas ta Tsakiya.

Steinmeier, ya kara da cewa, duk da wadannan kalubalen da ake fuskanta yana da yakinin al'amura za su daidaita tare da fatan magance su a shekara mai kamawa.

Dangane da al'amuran da suka shafi cikin gida a kasar ta Jamus, shugaban kasar duk da bai bayyana su ba kai tsaye, ya ce suna da masaniyar abubuwan da ke faruwa kuma yana da tabbacin cewa za su karfafa dimukuradiyya tare da jaddada bukatar aiki tare.

Shugaban na Jamus ya karkare da cewa, jami'an 'yan sanda da  na kashe gobara da sojoji da jami'an kiwon lafiya da dukkan ma'aikata sun cancanci jinjina wajen tabbatar da Jamus din da kowa yake fata.