1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan Bin Laden ya haddasa rikicin siyasa a Pakistan

May 9, 2011

Majalisar dokokin Pakistan ta buƙaci Firaminista ya yi bayani game da harin Amurika da ya hallaka Osama Bin Laden

Barack ObamaHoto: ap

Firaministan Pakistan ya baiyana gaban 'yan majalisar dokokin ƙasar domin bada bahasi akan harin da sojojin Amurika suka kai a gidan Osama Ben ladan da ke Abbotaba kusa da babban birnin ƙasar wato Islamabad wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sa mako guda da ya wuce.

Bayanar ta Firaminista gaban wakilan al'ummar ta zo a daidai lokacin da 'yan adawa a ƙasar ta Pakistan da kuma Amurika suke zargi hukumomi ƙasar da nuna gazawa sannan ma da hasashen haɗin kai da ake yi cewa suna baiwa jagoran 'yan ta'adar Osama Bin Laden.Kuma Allah kuli hali masu lura da al'amura na tunani cewa martaba da ƙimar gwamnatin ta Gilani na ƙara zubewa a idanuwa 'yan ƙasar da ke kallon cewa ana yi masu azarɓaɓi a masayin su na ƙasa mai cikkaken yanci.

Osama Bin LadenHoto: AP

Galibi jama'ar ƙasar na nuna adawa tun farko da hare haren da ƙungiyar CIA ke kaiwa cikin jirage mara sa matuƙa a sanssani 'yan taliban tun kafin ma wannan hari da ya kashe Osama.

Kuma da alama hukumomin na Pakistan sun shiga tsaka mai wuya daga 'yan ƙasar da kuma Amurka akan wannan zance.

Wanda shugaba Barack Obama ya ce tilas hukumomin Pakistan su sanar da su abinda ya faru ta yadda Osaman ya ƙwashe shekaru biyar ya na zaune a ƙasar amma kuma ba tare da sun sanar ba abinda ya kai ga zargin da suke yi cewa a kwai lauje cikin naɗi.

Shugaban Amurka ya ce suna tsammani kamar akwai waɗanda ke baiwa Osaman goyon bayya a Pakistan sai dai kawo yanzu basu san ko daga wane ɓangare ba ne ya ke samu haɗin kai walau daga wasu yan ´ƙasar ko kuma daga gwamnati.

Biri dai ya yi kama da mutun kuma tun tuni da wasu man 'yan jami'an gwamnatin Amurka basu yi wata wata ba wajan cewa ƙarara Hukumin Pakistan ɗin suna da masaniya dangane da zaman Bin Laden, Donilon wani mashawarcin shugaba Obama ya ce ya kamata tun da farko su bamu bayyanai na siri kuma ba wani tabbaba da waɗannan mata guda ukku na Osama da ake tsare da su za a daɗa samun haske.

Tarin kasset da bideo da kuma faya fayen naɗar bayyanai da aka samu a gidan Bin laden na iya zama wata babbar hanyar gudanar da bincikken da zai iya kai Amurka ta tantance alaƙa jagoran 'yan ta'adar da duka wasu bangarori da ake zargi.

Sai dai kuma ayyar tambayar da manazarta ke azawa shine wacce irin hulɗa za a ci gaba da yi tsakanin Amurika da Pakistan idan har aka gano cewar ta na da masaniya akan maɓuyar Osaman ko kuma shi fraministan ya fito ya baiyana haka.

Yousuf Raza Gilani, a gaban MajalisaHoto: picture-alliance/dpa

Tsofon Mataimakin shugaban Amurika Dick Cheney ya ce Amurka ta yi hattara wajan gaggauta yanke hukumci.

Idan muka samu rarabuwar kawunan wajan tafiya tare da ƙasashen Pakistan da Afganistan ina da fargaba akan kasawar da mu kan iya cimma akan sha'anin yaƙi da ta'adanci ya kamata mu tafiyar da kyaukyawar hulɗa tsakanin mu da waɗannan ƙasashe.

Pakistan na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka biya da tsada akan ɗamara yaƙii da ta'adanci da ƙungiyar Aqaida da amurka ta shiga yi tun a shekara ta 2001.Kawo yanzu sojojin ƙasar sama da dubu biyar ne suka mutu akan iyaka da Afganistan a cikin faɗa da 'yan Alqaida da kuma 'yan taliban.kuma Komi ta ke zama dai a jawabi da framinstan zai yi a gaban majalisar ba zai hanna jadada gabatar da buƙatar da 'yan adawar suka yi ba na marabus din shugaban ƙasar Asif Ali zardari tare da fraministan sa dagane da abin kumyar da suke zargin gwamnatin da aikatawa

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar