1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Boko Haram ta kashe ma'aikatan agaji

July 23, 2020

Mayakan Boko Haram sun yi wa wasu ma'aikatan agaji hudu da wani jami'in tsaro guda kisan gilla, bayan sun yi garkuwa da su.

Nigeria 65 Menschen von Islamisten der Gruppe Boko Haram getötet
Boko Haram na ci gaba da kashe mutane a Arewa maso Gabashin NajeriyaHoto: AFP/A. Marte

Ofishin kula da ayyyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya da da gwamnatin Tarayyar Najeriya tare da 'yan uwa da abokan arziki da ma sauran al'umma dai, sun yi Allah wadai da wannan kisa. Duk da cewa wannan ba shi ne karo na farko da mayakan na Boko Haram wadanda ke alaka da Kungiyar ISIS ke halaka ma'aikatan agajin da suka kama suka yi garkuwa da su a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar ba, amma na wannan karon ya tayar da hankulan al'umma musamman ganin yanayin da aka halaka sun. Bisa wannan ne bangarorin al'umma ke nuna takaici da bakin ciki na yadda ba a iya ceto wadannan bayin Allah ba, wadanda a baya aka nuna su a wani faifen bidiyo da kungiyar ta fitar suna rokon a fanshi rayukansu daga hannun mayakan.

'Yan gudun hijira na bukatar agajiHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Tuni dai ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da harkokin jin kai a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar, ya fitar da wata sanarwa da ke nuna alhini da takaici kan kashe ma'aikatan agajin. Ita ma a nata bagaren gwamnatin Tarayyar Najeriyar ta nuna takaicinta kan kisan gillar da aka yi wa ma'aikatan agajin, tare da yin alwashin nemo wadanda suka yi kisan domin hukunta su kamar yadda doka ta tanadar. Sai dai a cewar wasu daga cikin iyalan, gwamnatin ba ta nuna damuwa ko yin kokari na ceto 'yan -uwan nasu ba har ta Allah ta kasance da su. Sauran masu aikin jin kai a wadannan yankunan sun ce kisan ba zai kashe musu gwiwa a kokarinsu na taimakawa jama'a ba, sai dai dole a samu gibi a ayyukan agajin.

Masu fashin baki kan harkokin yau da kullum kamar Muhammad Matawalle Doka na ganin wannan kisan gilla a matsayin babbar barazana ga tsaro da ma ayyukan na jin kai. Babbar damuwa da masu aikin jin kai suka shiga a wannan yanin shi ne, barazanar da kungiyar ta Boko Haram ta yi na cewa za  ta ci gaba da kame su tare da halaka su, abin da ake ganin ka iya sanya wasu da dama yin watsi da ayyukan agajin a daidai lokacin da ake ci gaba da samun masu bukatar agajin gaggawa a yankin.