1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan kashoggi ya bar baya da kura

Abdullahi Tanko Bala
October 25, 2018

Saudiyya tace a shirye take ta hukunta wadanda ke da alhakin kisan dan jaridar nan Jamal Kashoggi tana mai siffantasu da jami'an tsaro da suka wuce gona da iri.

Dschamal Chaschukdschi
Hoto: Getty Images/AFP/M. Al-Shaikh

Hukumomin kasar Saudiyya sun ce bincike da ake gudanarwa game da kisan dan jaridar nan Jamal Kashoggi wanda ya mutu a ofishin jakadancin Saudiyya a Turkiyya zai bankado gaskiyar al'amuran da suka faru.

Ministan harkokin wajen Saudiyyar Adel al Jubeir wanda ya baiyana hakan ya jaddada kudirin gwamnatin Saudiyya na tabbatar da cikakken bincike da zai baiyana gaskiya.

Shi ma yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya yi alkawarin hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu a kisan dan jaridar. 

 


 

 

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna