1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Kisan Kiyashi na farko a ƙarni na 20 a Namibiya

April 8, 2024

A tsakanin shekara ta 1904 zuwa ta 1908, ‘Yan Mulkin Mallakar Jamus sun aikata kisan kiyashi kan al’ummar Herero da Nama da ke Namibiya. Wannan lamari har zuwa yau, yana ci gaba da zama batun muhawara a Namibiya.

Malkin mallaka na Jamus a Afirka
Malkin mallaka na Jamus a AfirkaHoto: Comic Republic


Ta Yaya Mutanen Hereros suka samu cuɗanya da Jamusawa?

Bayan da aka kafa iyakokin yankunan Kudu Maso Yammacin Afirka, ƙarƙashin ikon Jamus, sai hukumomin Jamus suka mayar da yankin na Jamusawa ‘yan kama wuri-zauna, ba kamar waɗansu yankunan mallakar Jamus ba a Afrika. Daga nan sai ‘yan kama-wuri-zauna suka fara kwararowa yankunan gaɓar Lüderitz da Swakopmund. Mahukuntan mulkin mallaka na Jamus suna ganin yankin zai dace da kiwon dabbobi. Ba a daɗe ba sai Jamusawa ‘yan kama-wuri-zauna suka fara artabu da mutanen Nama da na Herero.

Yaya dangantakarsu take tun farko?

Da farko dai, dangantakar da ke tsakanin Jamusawa da mutanen Herero kyakkyawa ce, har ma wasu mutanen Herero suka koma Addinin Kirista, kuma suka yi maraba da zaman Jamusawa. Haka kuma sun ƙulla yarjejeniyar kariya da ‘yan mulkin mallakar a kan kare su daga farmakin abokan hamayyarsu mutanen Nama.

A zahiri, dukkan ɓangarorin biyu sun kai wa juna farmaki. Mutanen Nama da na OvaHerero sun sanya hannu a kan yarjejeniya da Jamus kuma dukkan al’ummomin biyu sai suka rasa tasirin da suke da shi da shanunsu da kuma gonakinsu ga ‘yan mulkin mallaka.

Waɗanne abubuwa ne suka Jawo rikicin?

A 1897, annobar cutar shanu ta hallaka dabbobi masu yawa, waɗanda suna da muhimmanci ga tattalin arziƙin mutanen Herero, da ma mutane gaba ɗaya. Daga wajejen shekara ta 1903, Jamusawa 5,000 ne suke zaune a wannan Gundumar Mulkin Mallaka, amma kuma suna buƙatar manyan gonaki da za su yi noma. Hukumomin 'yan mulkin mallaka sun yi la'akari da wannan buƙata, don haka sai suka yi amfani da dabaru daban-daban wajen raba mutanen OvalHerero da gonakinsu da kuma shanunsu, ko da kuwa hakan ya haɗa da saɓa wa yarjejeniyar da aka ƙulla. Nuna wariyar launin fata da bambanci ta fuskar doka tsakanin ‘yan ƙasa da Jamusawa ‘yan kama wuri-zauna da kuma cin zarafin mutanen Herero da Nama cikin gonakin da Jamusawa suka mallaka, ya jawo wutar rikicin ta daɗa ruruwa. Wani hukunci mai sauƙi da aka yi wa wani Bajamushe ɗan kama-wuri zauna, wanda ya yi wa wata ‘yar ɗaya daga cikin sarakuna fyaɗe kuma ya kashe ta, ya fito da wannan cin zarafi a fili.

A cikin shekarar 1904, dakarun OvaHerero sun kashe sama da Jamusawa ‘yan kama wuri-zauna 100. Wannan bore ko kuma matakin soja na ƙwato iko a kan yankuna, kamar yadda shugabannin Herero suke kallon abin, ya zama kamar wani saƙo mai tayar da hankali da ya isa har birinin Berlin.

Tunawa da kisan kare dangi a NamibiyaHoto: Java

Wane abu ne ya tunzura rikicin?

A tsakiyar shekarar 1904, Janar Lothar von Trotha, ya karɓi jagoracin dakarun Jamus, inda sojojin Jamus, ko rundunar Schutztruppe, suka kwarara cikin wannan gunduma ta mulkin malaka. Kamar yadda Von Trotha ya faɗa da bakinsa, shi ba wai nasara yake so ya samu a kan Mutanen OvaHerero ba, so yake ya murƙushe su. Nan da nan kuwa sai sojojinsa da ke ɗauke da makamai suka kewaye dakarun OvaHerero a yankin Waterberg, inda suka karya lagon mutanen Herero na yin faɗa.

A wace gaɓa ce Rikicin ya rikiɗe zuwa kisan kiyashi?

Wannan doka ta hallaka su cewa take, duk wani ɗan Herero da aka same shi a yankin da Jamusawa suke zaune to a kashe shi. Don haka sai aka kori mutanen OɓaHerero zuwa hamadar Omaheke, wadda Hamada ce mai faɗi da ta faɗa har cikin ƙasar Botswana, wadda kuma take da ƙarancin wuraren samun ruwa.

Ba a da tabbacin alƙaluman waɗanda suka mutu, amma an ƙiyasta cewa kusan mutanen OvaHerero 80,000, maza da mata da yara ƙanana ne suka mutu. Wato kashi 75 cikin 100 ke nan na yawan mutanen Herero a wannan lokacin, inda da farko abin ya fara ne ta hana su abinci, daga nan kuma sai yunwa, da saka su aiki mai tsanani a cikin sansanin fursunonin yaƙin Swakopmund da na Lüderitz, masu sanyi da Hamada. Wasu mutum 10,000 kuma daga cikin mutanen Nama su 20,000 su ma sun mutu a lokacin mulkin mallaka. Idan aka kwatanta da sojojin Jamus, waɗanda suka mutu ba su kai mutum 1,000 ba.

Zanga-zanga kan yarjejenyiar Jamus bisa kisan kare dangi a NamibiyaHoto: Sakeus Iikela/DW

Me ya sa har yanzu ake labarin wannan rikici da kuma kisan kiyashi da aka yi?

An tarwatsa mutanen Herero da na Nama zuwa Kudancin Afrika, waɗanda kuma suka tsaya a gundumar mulkin mallaka ta Jamus, sun fuskanci tursasawa ta neman aiki a gonakin da garuruwan Jamusawa. Waɗannan gonaki da aka ƙwata an bayar da su a matsayin mallaki na ‘halaliya’ kuma an ba da su ko kuma an sayar da su ga ‘yan kama-wuri-zauna da kuma sojojin mulkin mallaka. Bayan shekara 100 kawo yanzu, yawancin waɗannan gonaki suna hannun ‘yan Namibiya waɗanda asalinsu Jamusawa ne.

A wani furucin yarjejeniyar ƙasa da ƙasa da aka ƙulla a 2021, ta bayyana cewa Jamus za ta ba wa gwamnatin Namibiya Yuro biliyan €1.1 (wato dala biliyan $1.16) a cikin shekaru 30.

Ko Jamus ta biya diyya?

Sam. Duk da cewa Jamus ta nemi afuwa a kan wannan laifi da ta aikata, wanda a fahintar wannan lokaci za a ɗauke shi a matsayin kisan kiyashi, ba ta amince cewa abin da ya faru a tsakanin shekarar 1904-1908 a matsayin kisan kiyashi ba ne, ta fuskar shari’a, wanda hakan na nufin ba za a sa Jamus ta biya diyya ba.

Ta yaya shugabannin Nama da Herero suka mayar da martani?

Sun ce su ba a tuntuɓe su ba, kuma ba a shigar da su cikin tattaunawar da aka yi ba, domin yarjejeniyar ta shafi Jamus ne da gwamnatin Namibiya kaɗai, ban da mutanen

da abin ya shafa. A watan Janairu saboda ta saɓa da tanade-tanaden tsarin mulkin Namibiya.2023, lauyan da ke wakiltar mutanen Nama da OvaHerero, ya yi kira da a rusa wannan yarjejeniya tsakanin Jamus da Namibiy,