Kissar mayaƙan alƙa'ida a Yemen
April 22, 2012Ma'aikatar kula da harkokin tsaro a ƙasar Yemen ta faɗi a wannan Lahadin cewar wani samamen da aka ƙaddamar a garin Loder dake kudancin ƙasar ya yi sanadiyyar mutuwar mayaƙa 17 da ake zaton 'yan ƙungiyar alQaeda ne. A cewar sanarwar da ma'aikatar ta fitar, wannan ya kawo adadin mayaƙan ƙungiyar da ta kashe a kwanaki ukkun da suka gabata ya zuwa 57, ko da shike kuma babu wata ƙafa mai zaman kanta da ta tantance sahihancin labarin. Hakanan ba'a kaiga sanin ko sojojin saman gwamnatin Yemen ne suka kai samamen da jiragen yaƙin su ko kuma sojojin Amirka ne suka kai farmakin da jiragen da basu da matuƙa.
A ranar larabar da ta gabata ce jaridar Washington Post da ake bugawa a Amirkar ta ce Samame ɗai-ɗai - har sau takwas ne jiragen yaƙin Amirka dake sarrafa kansu da kansu suka kai a Yemen cikin tsukin watanni huɗun da suka gabata. Mayaƙan dake tada ƙayar baya dai na ta ƙoƙarin ƙwace iko da garin Loder dake lardin Abyan domin faɗaɗa yankunan da suke da iko akan su a ƙasar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas