Nijar: Ko alaka za ta inganta da Benin?
April 24, 2026
Zababben shugaban kasar ta Benin dai ya yi wasu kalaman cewa, abin da ya fi shi ne a fuskanci juna domin rashin yin hakan ba zai magance matsaloli ba. A nasu bangaren hukumomin Jamhuriyar Nijar na ganin babbar matsalarsu da Benin ita ce, kasancewar sojojin Faransa. Koda yake wasu na ganin cewa Benin kasa ce mai 'yanci da ke iya hulda da wanda taga dama.
Yiwuwar cikar burin al'umma?
Tun dai farkon wannan matsala kungiyoyin fararan hula kamar FCR da Oumarou Souley ke jagoranta, sun sha jaddada kiransu ga bangarorin biyu kan su dubi al'umma su daidata hulda a tsakaninsu. A cewarsa, a yanzu idan har Benin ta bayar da tabbaci ga Nijar ya kamata ita ma Nijar ta duba lamarin. Masu iya magana dai na cewa, mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.
Wahalhalu ga mazauna kan iyaka
Ga mutanen da ke rayuwa a kusa da iyakokin kasashen Nijar da Benin da Nijar da Najeriya, su kadai suka san halin da suke ciki. Masana na da ra'ayin cewa abun jira a gani dai shi ne, matakin da Sabon shugaban na Benin Wadagni zai dauka, na ganin ya shirya da makwabtansa na yankin Sahel da su kansu makwabtan nasa ya kamata su yi don lamura su daidaita al'umomi su samu sassauci na rayuwa.
Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar