1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Zaben Zimbabwe darasi ga MDC

Privilege Musvanhiri
August 3, 2018

A daidai lokacin da al'ummar Zimbabuwe suka zabi sabon shugaban kasa daga jam'iyyar ZANU-PF yanzu lokaci ne da ya kamata 'yan adawa su koma kan tebur su sake yin karatun ta natsu

Simbabwe Wahlen Nelson Chamisa Anhänger
Hoto: Reuters/S. Sibeko

Wakilin tashar DW a Zimbabuwe Privilege Musvanhiri a cikin wannan sharhi da ya rubuta. Ya fara da cewa mai yiwuwa an yi aringizon kuri'u amma gaskiyar magana ita ce jam'iyyar MDC ba ta shiga zaben da kyakkyawan shiri ba. Kuri'u kusan dubu 550 da ta samu a babban birni Harare idan aka kwatanta da kimanin dubu 205 da ZANU-PF ta samu ya sa 'yan adawa sun rena matsayin jam'iyyar mai jan ragamar mulki, wadda tun bayan samunn 'yancin kai daga Birtaniya ta mamaye fagen siyasa. Karfinta dai ya faro tun daga tushe. A kauyukan da ke arewacin kasar ZANU-PF ta samu yawan kuri'u fiye da dubu 366, MDC ta samu dubu 97.

Dubarun siyasa na MDC ba su ba da la'akari da goyon bayan da ZANU-PF ke da shi bisa al'ada ba, domin ta san yadda za ta hada kan mutane su goya mata baya. Tana da kuma dadadden suna na tursasawa da tashin hankali.

Privilege Musvanhiri, wakilin DW a ZimbabweHoto: Privilege Musvanhiri

'Yan adawa sun sami isasshen lokacin tun bayan zaben 2013 su matsa kaimi domin aiwatar da canje-canje, amma sun gaza wajen kafa kansu a kasa ko a majalisa. Amma sai a 2018 suka mayar da hankali kan kurakuran jam'iyyar da ke mulki don su ci zabe. Manufofin yakin neman zabe jam'iyyun MDC da ZANU-PF sun mayar da hankali kan batutuan tattalin arziki da samar da aikin yi da abubuwan more rayuwa da dai sauransu. Yayin da ZANU-PF ta yi ta kira ga masu zabe da su fita zabe su kada mata kuri'a, ita kuwa MDC sakonninta ba su yi bayani karara ba, a wasu lokutan ma sun rikitar da masu zabe ne.

Rarrabuwar kai tsakanin 'yan adawa ta taka rawa wajen gazawarta. Manufarta ita ce ta shiga zaben a matsayin kawancen MDC, amma kanta bai hadu ba har ranar jajiberen zaben. Ana kuma zargin babu dimukaradiyya a tsare-tsarenta na cikin gida, ta kuma yi watsi da shi lokacin zaben fidda gwani.

Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Wadannan na daga cikin matsalolin MDC din da suka bude wa ZANU-PF gurbi, duk da ita ma kanta ta fuskanci matsaloli lokacin zaben fidda gwamni, amma ta yi kokari ta hada kan 'ya'yanta ta shiga zabe a matsayin tsintsinya madaurinki daya.
Yanzu dai ZANU-PF ta sake samun wata dama ta sake gina kasar da ta ruguza da kanta. A nata bangaren jam'iyyar MDC za ta koma ta yi karatun ta-natsu don ta tinkari zaben 2023 a matsayin jam'iyya mai karfi.

Bai kamata Zimbabuwe ta ci gaba da zama saniyar ware a duniya ba. Tana bukatar shugaban da zai dinke barakar da ke tsakanin 'yan kasar, wanda zai yaki cin hanci da rashawa, wanda kuma zai samar da kyakkyawan yanayi ga bunkasar tattalin arziki. 'Yan kasar sun zabi Emmerson Mnangagwa da ya yi wannan jagora. Nelson Chamisa da ke zama matashi ya karfafa fata cewa zai sake dawo a shirye da kuma karfi a zabe na gaba.