Zanga-zangar Morocco za ta shafi gasar AFCON ?
October 7, 2025
Za a fara kece raini tsakanin kungiyoyin kwallon kafa tsakanin Afirka daga ranar 21 ga watan Disamba na shekarar 2025 zuwa 18 ga watan Janairu na 2026, Moroko ta ware filaye guda tara da za a gudanar da wasannin.
Kasashen Afirka 24 za su fafata a gasar AFCON ta bana, kuma dan wasan gaba na Masar da Liverpool Mohamed Salah da dan wasan baya na Morocco da Paris Saint-Germain Achraf Hakimi na cikin 'yan wasan da za su taka leda a gasar bana.
Da alama shirin gasar na fuskantar barazana daga matasan Morocco, wadanda suka fito kan tituna don gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen cin hanci da rashawa da kuma sauya gwamnati kan abinda suka kira rashin adalci a bangarorin kiwon lafiya da kuma ilimi.
Da yake magana yayin taron shekara-shekara na shugabannin kwallon kafa na Afirka a Kinshasa, shugaban CAF Motsepe ya ce: "Hukumar CAF na da kwarin gwiwar cewa za a yi gasar kamar yadda aka tsara." Ya kara tabbatar wa hukumar FIFA cewa "CAF za ta nemi hadin kan gwamnati da dukkan 'yan kasar Maroko don karbar bakuncin gasar AFCON mafi nasara a tarihi."
Morocco ta karbi bakuncin gasar AFCON a shekarar 1988, sannan ta yi gasar kasashe takwas kuma ta rasa nasarar karbar bakuncin gasar a 2015 saboda fargabar cutar Ebola.
Shugaban CAF din Motsepe ya gaji tulin bashi lokacin da ya gaji shugabancin hukumar daga Ahmed Ahmed a 2021 bayan FIFA ta dakatar da Malagasy saboda keta ka'idojin da suka shafi aminci da cin zarafi da kuma karkatar da kudade.
Motsepe ya inganta hukumar cikin sauri har ta samu ribar dala miliyan 9.48 na shekarar 2023 zuwa 2024. CAF ta yi hasashen za a samu rarar dala miliyan 28.45 a shekarar 2026. "Mun samu gagarumar nasara a cikin shekaru biyar da suka gabata, kudaden shiga sun ninka sau hudu, babban abin da ya ba ni nasara a shugabancin hukumar shi ne salon yaki da da cin hanci da rashawa." in ji shugaban.
Gasar cin kofin nahiyar Afirka wanda aka kara fiye da sau 30 tun bayan fara gasar a shekarar 1957, Masar ce kasar da ta fi samun nasarar lashe kofin. Masar ta lashe wasan karshe har sau bakwai, ta yi nasara a jere a shekarun 1957 da 1959 sannan a 2006 da 2008 da kuma 2010.
Kasashen Kamaru da Ghana sun lashe kofin sau hudu ko sama da haka, inda ‘yan wasan kasar Ghana ke da bambancin tsallakewa zuwa zagayen karshe sau biyar fiye da kowacce kungiya duk da rashin nasara sau biyar.
Wasannin karshe da suka fi zira kwallaye a tarihin gasar sun gudana ne a shekarar 1957 karawar farko da Masar ta doke Sudan da ci 4-0 da kuma kece renin da aka yi a 1962 inda Habasha ta doke Masar da 4 da 2.