1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu: Za a zabi shugaban kasa

Abdourahamane Hassane
June 10, 2024

A Afirka ta Kudu a ranar Jumma'a aka shirya wakilai 400 da aka zaba a zaben 'yan majalisar dokoki.Za su yi zaman farko na majalisar a birnin Cape wanda akan zaman ne, za a zabi shugaban kasa.

Hoto: Kyodo/picture alliance

A karshen watan Mayu aka gudanar da zaben yan majalisar wanda a karon farko tun bayan zuwan mulkin demokaradiyya a kasar a shekara ta 1994. Jam'iyyar ANC mai mulki ta rasa rinjaye a majalisar wanda sai ta nemi kawance a yanzu da sauran jam'iyyun domin kafa gwamnati. Kamar yadda kundin tsarin mulkin na Afirka ta Kudu, ya tanada, dole ne a zabi shugaban majalisar, da mataimakinsa da kuma shugaban kasar a lokacin zaman majalisa na farko bayan zaben. Shugaban kasar na yanzu Cyril Ramaphosa, mai shekaru 71, na neman wa'adi na biyu. Sai dai kawo yanzu babu tabbas, ko zai wuce amma dai kawo yanzu  jam'iyyarsa na tattaunawa da sauran jam'iyyun siyasa don kafa gwamnatin.