1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ko dan takarar NDC zai kai bantensa?

September 18, 2026

A yayin da ake kara kusantar babban zaben Tarayyar Najeriya, gangamin OK na jam'iyyar NDC ya kaddamar da wani kwamitin tabbatar da zaben Peter Obi.

Najeriya | Peter Obi | Takara | NDC | Shugaban Kasa
Dantakarar jam'iyyar NDC a Najeriya Peter ObiHoto: Musa Tijjani Ahmad/DW

To sai dai kuma kama daga tsohon mikin basasa a sashen arewacin kasar ya zuwa adawar cikin jiharsa ta Anambra dai, daga dukkan alamu Peter Obi ya na da babban aiki kan hanyar karbe ikon da masu tsintsiyar ke jagoranta a halin yanzu a Najeriyar. Kwamitin na mutane 59 dai, na zaman gada tsakanin Obi da fadar mulki ta Abuja.

Daurin gindi zai bayar da nasara?

Wannan ne karo na biyu a shekaru Hudu da tsohon gwamnan Anambran ke kokarin gwada sa'arsa, a cikin batun shugabancin Najeriyar. Obi da ke zaman daya a cikin mafiya karancin shekaru a tsakanin manyan 'yan takarar shugabancin Najeriya dai, na zaman na kan gaba a daukar hankalin fagen na siyasa. Ana ganin yana da daurin gindin manya a ciki da ma wajen kasar, wadanda ke da bukatar sauyi yanzu, ko bayan farin jini a tsakanin mabiya addinin Kirista da ke fushi da tsarin Musulum Musulum na masu tsintsiyar kasar.

Tattaunawa da Peter Obi

18:10

This browser does not support the video element.

To sai dai kuma duk da takama cikin farin jinin addinin dai, Obi na kuma fuskantar kalubale iri-iri da ke barazana ga kokarin cika burin nasa. Can a sashen arewacin kasar inda Obin ya zabi Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso cikin neman sa'a da kila ma farin jini tsakanin al'ummar yankin dai, har ya zuwa yanzu tsohon mikin yakin basasa na sama da shekaru 50 na tasiri a kokarin burge al'ummar. A yayin kuma da a Kudu maso Gabas ta Obin dai, shugabannin jiharsa ta Anambra ke neman zama kadangaren bakin tulu ga bukatar tasa.

Rikicin cikin gida ya addabi APC

Gwamnatin jihar ta fitar da wani dimbin bashin da ta ce, gwamnatin Obi ta bari a kokarin nuna baikensa a fagen na siyasa. To sai dai kuma ko ya zuwa ina Obi ke iya kai wa a kokarin gwada sa'ar dai, dan takarar na jam'iyyar NDC daga dukkan alamu na cikin wani rikicin cikin gida da ke barazanar tsinke tsintsiyar APC da ya gwara kan tsakanin 'ya'yan gado da agololin da ke tunanin karbe gida. Sannu a hankali dai, APC na ganin dada zurfin rikicin da ke tsakanin Nyesom Wike da gwamnonin jam'iyyar.

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW